Surat Ibrahim, aya ta 22

14:22

وَقَالَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَمَّا قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ إِنَّ ٱللَّهَ وَعَدَكُمۡ وَعۡدَ ٱلۡحَقِّ وَوَعَدتُّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُكُمۡۖ وَمَا كَانَ لِيَ عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّآ أَن دَعَوۡتُكُمۡ فَٱسۡتَجَبۡتُمۡ لِيۖ فَلَا تَلُومُونِي وَلُومُوٓاْ أَنفُسَكُمۖ مَّآ أَنَا۠ بِمُصۡرِخِكُمۡ وَمَآ أَنتُم بِمُصۡرِخِيَّ إِنِّي كَفَرۡتُ بِمَآ أَشۡرَكۡتُمُونِ مِن قَبۡلُۗ إِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ ٢٢

Waqālash-shaytānu lammā qudiyal-amru innallāha wa'adakum wa'dal-haqqi wawa'attukum fa akhlaftukum wamā kāna liya 'alaykum min sultānin illā an da'awtukum fastajabtum lī falā talūmūnī walūmū anfusakum mā ana bimusrikhikum wamā antum bimusrikhiyya innī kafartu bimā ashraktumūni min qablu innaz-zālimīna lahum 'adhābun alīm

Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, "Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini. Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da shi gabanin wannan (matsayi). Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi."1

Bayanan ƙasa

1 Huɗubar Shaiɗan ga mabiyansa, a cikin wuta, a bãyan an yi muhãwara a tsakãnin mabiya da shugabannin kãfirci, sãshe yanã la'antar sãshe har abu ya kai ga Shaiɗan, watau Iblis. Shi kuma ya tãshi ya yi wannan huɗuba dõmin ya ƙãra musu baƙin ciki a kan wani.