Surat At-Talaq, aya ta 11

65:11

رَّسُولٗا يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ مُبَيِّنَٰتٖ لِّيُخۡرِجَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَيَعۡمَلۡ صَٰلِحٗا يُدۡخِلۡهُ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ قَدۡ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ لَهُۥ رِزۡقًا ١١

Rrasūlan yatlū 'alaykum āyātillāhi mubayyinātil liyukhrijal-ladhīna āmanū wa'amilus-sālihāti minaz-zulumāti ilan-nūri waman yu'mim billāhi waya'mal sālihan yudkhilhu jannātin tajrī min tahtihal-anhāru khālidīna fīhā abadan qad ahsanallāhu lahū rizqā

Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata1 masa arziki.

Bayanan ƙasa

1 Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: "Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa (mai tsare sharĩ'ar) arziki," bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba.