Surat At-Tahrim, aya ta 8

66:8

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ تُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ تَوۡبَةٗ نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيُدۡخِلَكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يَوۡمَ لَا يُخۡزِي ٱللَّهُ ٱلنَّبِيَّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥۖ نُورُهُمۡ يَسۡعَىٰ بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَبِأَيۡمَٰنِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَتۡمِمۡ لَنَا نُورَنَا وَٱغۡفِرۡ لَنَآۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ ٨

Yā'ayyuhal-ladhīna āmanū tūbū ilallāhi tawbatan nasūhan 'asā rabbukum an yukaffira 'ankum sayyi'ātikum wayudkhilakum jannātin tajrī min tahtihal-anhāru yawma lā yukhzillāhun-nabiyya walladhīna āmanū ma'ahū nūruhum yas'ā bayna aydīhim wabi'aymānihim yaqūlūna rabbanā atmim lanā nūranā waghfir lanā innaka 'alā kulli shay'in qadīr

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi 1da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne."

Bayanan ƙasa

1 Allah Yã yi alkawarin bã zai kunyatar da AnnabinSa ba, haka kuma waɗanda sukayi ĩmãni tãre da shi, watau sahabbansa a Rãnar Kiyãma. Wannan shĩ ne dalĩlin da ya sa Allah Ya tsare Annabi da Sahabbansa daga bauta musu kamar yadda aka bautã wa waɗansu Annabãwa da Sãlihai waɗanda Allah zai tambaye su kõ sũ ne suka yi umurni da a yi musu bautar, sũ kuma su faɗi barrantarsu daga waɗanda suka bauta musu.