Surat Ar-Ra'd, aya ta 30

13:30

كَذَٰلِكَ أَرۡسَلۡنَٰكَ فِيٓ أُمَّةٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهَآ أُمَمٞ لِّتَتۡلُوَاْ عَلَيۡهِمُ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَهُمۡ يَكۡفُرُونَ بِٱلرَّحۡمَٰنِۚ قُلۡ هُوَ رَبِّي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ مَتَابِ ٣٠

Kadhālika arsalnāka fī ummatin qad khalat min qablihā umamul litatluwa 'alayhimul-ladhī awhaynā ilayka wahum yakfurūna bir-rahmāni qul huwa rabbī lā ilāha illā huwa 'alayhi tawakkaltu wa ilayhi matāb

Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman.1 Ka ce: "Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take."

Bayanan ƙasa

1 Sũnan Allah Rahmãn, daga rahama, watau Mai Rahama wadda yake dukan alheri yanã shiga a cikin ma'anarta a wajen halitta da rãyuwa da bãyar da lãfiya da shiryarwa. Mafi girman nĩ'imarsa shĩ ne aikõwar Manzon Allah daga gare mu zuwa gare mu. Kãfirai ba su yi tunãni ba a kan waɗannan rahamõmi, balle su yi gõdiya, sabõda haka sai kãfirci suke yi.