Surat Al-Qasas, aya ta 86

28:86

وَمَا كُنتَ تَرۡجُوٓاْ أَن يُلۡقَىٰٓ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبُ إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرٗا لِّلۡكَٰفِرِينَ ٨٦

Wamā kunta tarjū an yulqā ilaykal-kitābu illā rahmatam mir rabbika falā takūnanna zahīral lil-kāfirīn

Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako1 ga kãfirai.

Bayanan ƙasa

1 Taimakon, shi ne ka yi bũrin musuluntarsu har ka wahala dõmin a sauƙaƙe ma hukuncin hijira wadda Allah Ya yi umurni da a yi ta a bãyan musulunta sai ka iyar da Manzanci, shiryarwa kuwa ga hannun Allah take. Wannan ãyã tanã nunãwa bayyana ƙaryar mãsu da'awar cewa wani mutum yanã bai wa wani ĩmãni ko ya karɓe shi daga gare shi. Kõwa a cikin tsõro yake, sai wanda Allah Ya sanya shi cikin aminci. Allah Ya sanya mu cikin amincinSa dõmin rahamarsa.