Surat Al-Isra, aya ta 9

17:9

إِنَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ يَهۡدِي لِلَّتِي هِيَ أَقۡوَمُ وَيُبَشِّرُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرٗا كَبِيرٗا ٩

Inna hādhal-qur'āna yahdī lillatī hiya aqwamu wayubasshirul-mu'minīnal-ladhīna ya'malūnas-sālihāti anna lahum ajran kabīrā

Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita1 kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."

Bayanan ƙasa

1 Bãyan ya faɗi abũbuwan da Attaura ta karantar, ya ce: "Alƙur'ãni yanã shiryarwa zuwa ga hãlãyen da suka fi daidaita daga abin da Attaura ta karantar." Sa'an nan ya ci gaba da bayãnin abũbuwan da Alƙur'ãni yake karantarwa.