فَلَمَّا وَضَعَتۡهَا قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي وَضَعۡتُهَآ أُنثَىٰ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا وَضَعَتۡ وَلَيۡسَ ٱلذَّكَرُ كَٱلۡأُنثَىٰۖ وَإِنِّي سَمَّيۡتُهَا مَرۡيَمَ وَإِنِّيٓ أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ ٣٦
Falammā wada'athā qālat rabbi innī wada'tuhā unthā wallāhu a'lamu bimā wada'at walaysadh-dhakaru kal-unthā wa innī sammaytuhā maryama wa innī u'īdhuhā bika wadhurriyyatahā minash-shaytānir-rajīm
To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu1 kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe."
Bayanan ƙasa
1 Maryam, ma'anarta mai ibãda. Abinci da ake kai mata a cikin Masallaci shĩ ne 'ya'yan itãce, irin na ɗãri, a lõkacin bazara, kuma irin na bazara a lõkacin ɗãri. Wannan kuma ya mõtsar da begen zakariyya ga sãmun ɗã, bãyan shi da mãtarsa sun tsũfa ba su haifu ba. Sai ya rõƙi Allah kuma Ya karɓa masa, Ya ba shi Yahaya Annabi.