Surat Al-Baqarah, aya ta 40

2:40

يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِيٓ أُوفِ بِعَهۡدِكُمۡ وَإِيَّٰيَ فَٱرۡهَبُونِ ٤٠

Yābanī isrā'īladhkurū ni'matiyal-latī an'amtu 'alaykum wa awfū bi'ahdī ūfi bi'ahdikum wa iyyāya farhabūn

Yã Banĩ Isrã'Ĩla1! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.

Bayanan ƙasa

1 Bãyan kiran mutãne gabã ɗaya zuwa ga addinin musulunci, sai kuma ya keɓance Yahũdu da kira zuwa ga addinin, dõmin sun bambanta da sauran kãfirai, sabõda ilminsu ga gaskiyar Musulunci. Yã gabata cewa jama'ar, kashi huɗu ce; mũminai, da kãfiran Lãrabãwan da bã zã su musulunta ba, da munãfukai da Yahũdu. Ya kira Yahũdu da Bani Isrã'ĩla, dõmin Ya tunãtar da su, cewa anã kiransu ne zuwa ga addini irin na ubansu Ya'aƙũbu bawan Allah.